Menene Cryptocurrency???
MAI TAMBAYA: MENENE CRYPTOCURRENCY...?
AMSA: Ka ƙaddara a ranka crypto wani kuɗi ne na intanet, kamar dai yadda kuɗin takadda yake, sai dai kawai shi banbancinci da kuɗin takadda shine shi a intanet yake. A maimakon kuɗin takadda da gwamnatin ƙasa ke da iko dashi, to shi crypto yana aiki ne akan wani tsarin intanet mai ƴanci wadda ake kira da "Blockchain".
Akan wannan tsarin intanet ɗin na Blockchain ake ajiye bayanan komai na kuɗin crypto, duk wanda ka turawa kuɗin crypto konya turo maka idan aka duba zaayga wannan bayanan akan intanet na Blockchain. Tsarin intanet na Blockchain yana da tsananin tsaro fiye da normal intanet da muke dashi.
Banbancin tsarin Intanet na Blockchain da kuma Normal Intanet da muke amfani dashi shine: Misali kamar facebook yana kan normal intanet da muke amfani dashi, dan haka duk wanda yake amfani da facebook toh facebook suna da cikakken iko dashi.
Toh da ace facebook akan tsarin intanet na Blockchain yake toh facebook basu da wani iko dakai. Wannan dalilin yasa ake wa tsarin intanet na Blockchain laƙabi da "Intanet Mai Ƴanci", kana da damar yin komai naka ba tare da tsangwama ba.
"Idan nace iko ina nufin: Facebook nada ikon rufe ma account naka, restriction dinsa, hanaka comments dss"
Toh su wannan kuɗin crypto ɗin akan tsarin intanet na Blockchain aka gina su, shiyasa suma ake musu laƙabi da "Kuɗi Masu Ƴanci". A maimakon yanzu idan kana da kuɗi a bankinka, toh bankin nada iko dakai, toh su kuɗin crypto idan ka mallake su ka mallaka kenan ba wanda ya isa dasu in ba kai ba.
MAI TAMBAYA: TAYAYA KUƊIN CRYPTO SUKA ZAMA KUƊI DA HAR KAKE IYA CHANZA SU KA KARƁI NAIRA....?
AMSA: Kana ji yanzu idan na kirkiri kuɗin crypto akan Blockchain, da farko zan fara bashi adadi. Misali na kirkiri coin ɗin mai suna $ORC, dana tashi kirkirar sa sai na kirkiri guda 1Million. Toh da farkon lokaci dana kirkiri sa ba komai bane shi illa numbobi.
Lokacin da nake so ya zama kuɗi akwai hanyoyi guda 3 zuwa 5 da ake bi ya zama kuɗi, na 5 ɗin shine wanda yafi rikitarwa:
1. Na farko akwai abinda ake cewa ICO (Initial Coin Offering) ko kuma ace IPO (Initial Public Offering). Shi yadda tsarin yake shine: Zan dauki wannan coin ɗin nawa dana kirkira guda 1million mai suna $ORC, sai na bawa jama'ar gari dama akan su zo su sayi coin ɗin. Wannan kuɗin da zasuyi amfani dashi gurin siyan coin ɗin, shine kuɗin da zai zama abinda ake kira Liquidity.
"Liquidity: kowanne kuɗin crypto na buƙatar shi, Liquidity shine yake baka damar idan kana da kuɗin crypto ka iya chanza shi a baka Dollar ko Naira. Toh wannan kuɗin da ake karba na ICO shi ake amfani dashi guri Liquidity"
MAI TAMBAYA: TOH DAN ALLAH KAFIN KA TAFI NA 2, INA SON KA FAƊA MINI SU WAƊANDA SUKA SAYI COIN ƊIN A "ICO" TAYAYA SUKE CIN RIBA, KO KAWAI SAKAWA SUKE SHIKENAN KUƊIN SU YA TAFI A WOFI..?
AMSA: Shi kuɗin crypto yana hawa da sauka ne, misali idan na sayi coin a ICO yana kan a ƙaddara ₦10, to yayin daya shigo kasuwa mutane suka fara siye da siyarwa dashi. Farashin sa zai iya tashi ya zama ₦50, kaga kenan naci riba ko.
2. Bayan ICO, abu na biyu akwai abinda muke kira da IEO "Initial Exchange Offering", shima dai kamar ICO yake. Sai dai shi a maimakon zuwa da zakayi ka sayi coin direct ta hannun masu coin ɗin, shi IEO a kasuwannin crypto akeyin sa irin su Binance, Kucoin, CoinEx, Bitget dss.
3. Akwai kuma IDO "Initial Dex Offering".
"A crypto akwai tsarin gurin siyayya guda biyu, na farko akwai CEX "Centralized Exchanges" su gurin siyayya ne na crypto da suke aiki kamar banki, sai kayi KYC kayi komai kafin ka fara amfani dasu. Akwai kuma DEX "Decentralized Exchanges" asalin tsarin crypto kenan, shi kuma ba abinda ake buƙata kawai budewa zakayi ka fara amfani dasu"
Toh IDO anayin sa ne a gurin musayar crypto na DEX, shima duk yana aiki ne irin yadda ICO da IEO suke.
4. Sai kuma IFO "Initial Farming Offering", shi kuma sani tsari ne da akeyi wanda za'a ce ka sayi wani coin da tuntuni yana kasuwar crypto ka ajiye sa, za'a dinga baka wannan sabon coin ɗin da bai shigo kasuwa ba kyauta.
5. Sai na ƙarshe sanda yafi kowanne ruɗarwa shine IAO "Initial Airdrop Offering". Shi kuma coin ɗin ake rabawa kyauta ga mutane, amma fa dabara ce da ake amfani da ita dan tara mutane. Misalin irin wannan tsarin, akwai mining da mukeyi.
Suna dabara su tara mutane ta hanyar alkawarin zasu basu coin ɗin su kyauta, sai su ce musu suyi wani aiki. Lokacin da wa'adi ya cika, dama a chan gefe guda akwai wasu manya masu kuɗin crypto da kasuwanni da zasu ga. Ai project kaza yana da mutane da yawa.
Dan haka sai su dauki kudinsu su saka a matsayin Liquidity a sa coin ɗin a kasuwa, su kuma sai a basu wani adadi na coin ɗin, misali coin ɗin guda miliyan daya ne, sai a basu dubu 500k. Sai ace to a hankula zuwa wani lokaci zasu siyar da coin ɗin da aka basu.
MAI TAMBAYA: TOH SU TAYAYA AKE SUKE MAYAR DA WANNAN MAHAUKATAN KUƊAƊEN DA SUKE SAWA AKE BAWA MUTANE FREE...?
AMSA: Na faɗa muku cewa kuɗin crypto hawa yake da sauka ko? Toh mutane sune suke zama sanadin hawan nan nashi da sauka, yayi da suka dinga siya toh farashi zai tashi yayin da sukayi ta siyarwa toh farashi zai sauka.
Toh karka manta coin ɗin da akayi mining dole yana da mutane bila'adadin da suka san shi, dan haka akwai mutanen da muke kira da Traders da kuma Holders a crypto. Da zarar sun samu labarin coin ɗin zasu fara saka kuɗi, hakan zai sa ya dinga tashi.
Ta yiwu an saka shi a ₦100 duk guda daya, toh bayan Traders da Holders sun fara siya sai kaji farashin ya dawo ₦800. Su kuma wannan manyan masu kuɗin crypto da kasuwannin dama an basu guda dubu 500k, kamar yadda aka musu alkawari.
Sune suka saka masa kuɗi ya fito a farashin ₦100, kaga kenan idan suka siya a ₦100, sai dai ma su faɗi basu ci riba ba. Amma da sun tsaya yaje farashin ₦800, toh yanzu ya ninka musu kuɗin su x7. Kaga suna cikin riba.
Akwai coins da yawa a kasuwar crypto, yanzu haka akwai guda sama da dubu 30k. Dan haka babban abinda kowanne project na crypto suke nema shine a sansu, ba kuma za'a san su ba sai mutane sun san su. Hakane yasa suke neman mutane suyi mining ko task.
Yin wannan mining ɗin da task ne yake sawa duniyar crypto ta san project din, tunda maybe dubbunai ko miliyoyin mutane ke mining ɗin ko task. Dan haka da zarar ya fito, Traders da Holders na crypto suke fara siyansa. Wannan ke sawa farashin sa ya tashi.
Wallahu Ya'alamu....!
Zuwan Cryptocurrency Ya Canza Hanyar Tura Kudade
Zuwan Cryptocurrency ya canza hanyar da muke bi wajan tura kuɗaɗe ƙasashen waje (Cross-border payments).
Kafin zuwan crypto akwai platforms da yawa da muke amfani dasu wajan yin Cross Border payment, kamar irin su PayPal, Traditional Banks (Western Union) Da sauran su sosai.
To Amman amfani da Traditional Banks Yana da matsaloli sosai, wanda mutane suke shan wahala, kamar irin su:
1. Tsadar Fee da ake biya wajan turawa.
2. Daɗewa kafin kuɗin suje wajan da ake buƙata.
3. Matsalar ɗan tsakiya, wanda zai iya ganin abun da aka tura, kuma zai iya dakatar wa idan be gamsu ba.
Da zuwan crypto sai ya bamu Faster, cheaper, and more secure way to send money across borders...
Ya kamata Ku sani: Crypto Bawai yazo ne ya ruguje komai ba, wasu abubuwan yana shiga cikin su ne ya gyara yadda suke tafiyar da ayyukan su...
Abun da nake nufi shine, wasu suna tunanin yanzu kawai tunda crypto Yana offering Decentralised Payment system, To shikkenan duka wannan Bankunan da International Payments gateways da muke dasu zasu rufe ne shikenan an dena yi dasu, wasu sabbin sai su buɗe a jikin Crypto a dinga tafiya dasu..
"Wannan ba haka ba"
A halin yanzu kusan 99% Na Cross Border Payment sun yi Adopting Bitcoin a matsayin Payment alternative ga users ɗinsu...
Wanda idan kai user ɗinsu ne wanda kake buƙatar yin amfani da Crypto wajan tura kuɗi ko amsar kuɗi, zaka iya yi. Kuma zaka samu dukkan wani sauƙi da Crypto yake samar wa. kamar yadda zaka yi amfani da sauran Platforms da aka gina su akan Blockchain (Cheap, Faster, secured).
Cryptocurrency kamar irin su $XRP $BTC $XLM Da sauran su. Wanda su dalilin ƙirƙirar su shine yin hada Hadar biyan kuɗaɗe na kayayyaki a Duniya baki daya (Global Remittance)...
A halin yanzu Bankuna daga manya manyan ƙasashen Duniya sun amsa irin wannan Crypto ɗin a matsayin Medium of International Payments ɗinsu, kamar irin su Indiya, Russia, America, CHINA. Dss.
Don haka idan kana da ɗan uwan da kake turawa kuɗi ƙasan waje, ka dinga Amfani da Crypto ta cikin wannan Bankunan da Platforms.
Ko kuma Direct Ka tura masa ta wallet ɗin shi daga wallet ɗinka.
Da fatan an gane wannan!.

OvER Protocol I.e OvER Chain ⛓️________________________________________________
Me Ya Faru da SUI?
Lokacin da aka list SUI token a kasuwa (Mayu 2023), farashin ya yi tashi kaɗan amma ya faɗi cikin sauri saboda Mutane da dama sun samu token ta airdrop ko pre-sale.
Suka yita sayarwa nan da nan don su ci riba.
Bayan haka, SUI team suka ci gaba da haɓaka ecosystem, suka kawo grants, dApps, partnerships, Sannan suka Samar da (supply control) yadda baza'a yi dumping coin dinsu ba.
Sakamakon hakan, farashin SUI ya fara ɗan murmurewa daga baya, ko dayake ba sosai ba yadda mutane sukayi tsammani ba sai bayan Shekara 1 listings farashin yawuce inda ba'a yi tsammani ba.
Shin OVER Protocol za su bi wannan hanyar kuwa irin yadda SUI sukayi?
OVER Protocol suma sin fuskanci irin wannan abun Bayan listing, mutane da suka samu airdrop ko early allocations sun fara sayar da token, hakan ya sa farashi ya faɗi sosai.
OvER sunada Strong vesting plan (kamar yadda suka sanar) kuma abune mai kyau hakan.
Sunada Community da staking incentive, Testnet da dApps da ake fatan za su ƙarfafi amfani da OvER nan gaba kadan like 1 year coming.
Irin abin da ya faru da SUI yana iya faruwa da OVER — amma ba lallai ba saidai Idan team ɗinsu sun ci gaba da haɓaka ecosystem da ƙarfafa amfani da token din, suna da damar tafiar da OvER daga ƙasa har su kai matsayi mai kyau.
Abun cewa anan Shine OvER ba blockchain bane karami, Yanada tsarin rulling nodes, DOA, decentralisation, dApps, staking, farashin OvER zai yi Kyau da yardar Allah, OvER zaiyi appreciate munada burin suyi appreciate din price dinsa.
OvER Yanada Kyaun dazaka Iya masa deba na musamman ka ajiye Shi don holding, Ina Mai tababbatar maka OvER da Core ba abun wasa bane Ina Kara maimatawa OvER ba abun wasa bane.
A wannan Era din na blockchain ka Samu OvER ka ajiyeshi, kada Kaga farashinsa a kasa ka dauka basuda plan, ko basuda kudi A'a ba haka bane, Indai kana da hali Saka OvER a cikin rumbun holding dinka Not financial advice slowly but surely Insha Allah nothing is impossible in Crypto.

MAI TAMBAYA: MENENE CRYPTOCURRENCY...?
AMSA: Ka ƙaddara a ranka crypto wani kuɗi ne na intanet, kamar dai yadda kuɗin takadda yake, sai dai kawai shi banbancinci da kuɗin takadda shine shi a intanet yake. A maimakon kuɗin takadda da gwamnatin ƙasa ke da iko dashi, to shi crypto yana aiki ne akan wani tsarin intanet mai ƴanci wadda ake kira da "Blockchain".
Akan wannan tsarin intanet ɗin na Blockchain ake ajiye bayanan komai na kuɗin crypto, duk wanda ka turawa kuɗin crypto konya turo maka idan aka duba zaayga wannan bayanan akan intanet na Blockchain. Tsarin intanet na Blockchain yana da tsananin tsaro fiye da normal intanet da muke dashi.
Banbancin tsarin Intanet na Blockchain da kuma Normal Intanet da muke amfani dashi shine: Misali kamar facebook yana kan normal intanet da muke amfani dashi, dan haka duk wanda yake amfani da facebook toh facebook suna da cikakken iko dashi.
Toh da ace facebook akan tsarin intanet na Blockchain yake toh facebook basu da wani iko dakai. Wannan dalilin yasa ake wa tsarin intanet na Blockchain laƙabi da "Intanet Mai Ƴanci", kana da damar yin komai naka ba tare da tsangwama ba.
"Idan nace iko ina nufin: Facebook nada ikon rufe ma account naka, restriction dinsa, hanaka comments dss"
Toh su wannan kuɗin crypto ɗin akan tsarin intanet na Blockchain aka gina su, shiyasa suma ake musu laƙabi da "Kuɗi Masu Ƴanci". A maimakon yanzu idan kana da kuɗi a bankinka, toh bankin nada iko dakai, toh su kuɗin crypto idan ka mallake su ka mallaka kenan ba wanda ya isa dasu in ba kai ba.
MAI TAMBAYA: TAYAYA KUƊIN CRYPTO SUKA ZAMA KUƊI DA HAR KAKE IYA CHANZA SU KA KARƁI NAIRA....?
AMSA: Kana ji yanzu idan na kirkiri kuɗin crypto akan Blockchain, da farko zan fara bashi adadi. Misali na kirkiri coin ɗin mai suna $ORC, dana tashi kirkirar sa sai na kirkiri guda 1Million. Toh da farkon lokaci dana kirkiri sa ba komai bane shi illa numbobi.
Lokacin da nake so ya zama kuɗi akwai hanyoyi guda 3 zuwa 5 da ake bi ya zama kuɗi, na 5 ɗin shine wanda yafi rikitarwa:
1. Na farko akwai abinda ake cewa ICO (Initial Coin Offering) ko kuma ace IPO (Initial Public Offering). Shi yadda tsarin yake shine: Zan dauki wannan coin ɗin nawa dana kirkira guda 1million mai suna $ORC, sai na bawa jama'ar gari dama akan su zo su sayi coin ɗin. Wannan kuɗin da zasuyi amfani dashi gurin siyan coin ɗin, shine kuɗin da zai zama abinda ake kira Liquidity.
"Liquidity: kowanne kuɗin crypto na buƙatar shi, Liquidity shine yake baka damar idan kana da kuɗin crypto ka iya chanza shi a baka Dollar ko Naira. Toh wannan kuɗin da ake karba na ICO shi ake amfani dashi guri Liquidity"
MAI TAMBAYA: TOH DAN ALLAH KAFIN KA TAFI NA 2, INA SON KA FAƊA MINI SU WAƊANDA SUKA SAYI COIN ƊIN A "ICO" TAYAYA SUKE CIN RIBA, KO KAWAI SAKAWA SUKE SHIKENAN KUƊIN SU YA TAFI A WOFI..?
AMSA: Shi kuɗin crypto yana hawa da sauka ne, misali idan na sayi coin a ICO yana kan a ƙaddara ₦10, to yayin daya shigo kasuwa mutane suka fara siye da siyarwa dashi. Farashin sa zai iya tashi ya zama ₦50, kaga kenan naci riba ko.
2. Bayan ICO, abu na biyu akwai abinda muke kira da IEO "Initial Exchange Offering", shima dai kamar ICO yake. Sai dai shi a maimakon zuwa da zakayi ka sayi coin direct ta hannun masu coin ɗin, shi IEO a kasuwannin crypto akeyin sa irin su Binance, Kucoin, CoinEx, Bitget dss.
3. Akwai kuma IDO "Initial Dex Offering".
"A crypto akwai tsarin gurin siyayya guda biyu, na farko akwai CEX "Centralized Exchanges" su gurin siyayya ne na crypto da suke aiki kamar banki, sai kayi KYC kayi komai kafin ka fara amfani dasu. Akwai kuma DEX "Decentralized Exchanges" asalin tsarin crypto kenan, shi kuma ba abinda ake buƙata kawai budewa zakayi ka fara amfani dasu"
Toh IDO anayin sa ne a gurin musayar crypto na DEX, shima duk yana aiki ne irin yadda ICO da IEO suke.
4. Sai kuma IFO "Initial Farming Offering", shi kuma sani tsari ne da akeyi wanda za'a ce ka sayi wani coin da tuntuni yana kasuwar crypto ka ajiye sa, za'a dinga baka wannan sabon coin ɗin da bai shigo kasuwa ba kyauta.
5. Sai na ƙarshe sanda yafi kowanne ruɗarwa shine IAO "Initial Airdrop Offering". Shi kuma coin ɗin ake rabawa kyauta ga mutane, amma fa dabara ce da ake amfani da ita dan tara mutane. Misalin irin wannan tsarin, akwai mining da mukeyi.
Suna dabara su tara mutane ta hanyar alkawarin zasu basu coin ɗin su kyauta, sai su ce musu suyi wani aiki. Lokacin da wa'adi ya cika, dama a chan gefe guda akwai wasu manya masu kuɗin crypto da kasuwanni da zasu ga. Ai project kaza yana da mutane da yawa.
Dan haka sai su dauki kudinsu su saka a matsayin Liquidity a sa coin ɗin a kasuwa, su kuma sai a basu wani adadi na coin ɗin, misali coin ɗin guda miliyan daya ne, sai a basu dubu 500k. Sai ace to a hankula zuwa wani lokaci zasu siyar da coin ɗin da aka basu.
MAI TAMBAYA: TOH SU TAYAYA AKE SUKE MAYAR DA WANNAN MAHAUKATAN KUƊAƊEN DA SUKE SAWA AKE BAWA MUTANE FREE...?
AMSA: Na faɗa muku cewa kuɗin crypto hawa yake da sauka ko? Toh mutane sune suke zama sanadin hawan nan nashi da sauka, yayi da suka dinga siya toh farashi zai tashi yayin da sukayi ta siyarwa toh farashi zai sauka.
Toh karka manta coin ɗin da akayi mining dole yana da mutane bila'adadin da suka san shi, dan haka akwai mutanen da muke kira da Traders da kuma Holders a crypto. Da zarar sun samu labarin coin ɗin zasu fara saka kuɗi, hakan zai sa ya dinga tashi.
Ta yiwu an saka shi a ₦100 duk guda daya, toh bayan Traders da Holders sun fara siya sai kaji farashin ya dawo ₦800. Su kuma wannan manyan masu kuɗin crypto da kasuwannin dama an basu guda dubu 500k, kamar yadda aka musu alkawari.
Sune suka saka masa kuɗi ya fito a farashin ₦100, kaga kenan idan suka siya a ₦100, sai dai ma su faɗi basu ci riba ba. Amma da sun tsaya yaje farashin ₦800, toh yanzu ya ninka musu kuɗin su x7. Kaga suna cikin riba.
Akwai coins da yawa a kasuwar crypto, yanzu haka akwai guda sama da dubu 30k. Dan haka babban abinda kowanne project na crypto suke nema shine a sansu, ba kuma za'a san su ba sai mutane sun san su. Hakane yasa suke neman mutane suyi mining ko task.
Yin wannan mining ɗin da task ne yake sawa duniyar crypto ta san project din, tunda maybe dubbunai ko miliyoyin mutane ke mining ɗin ko task. Dan haka da zarar ya fito, Traders da Holders na crypto suke fara siyansa. Wannan ke sawa farashin sa ya tashi.
Wallahu Ya'alamu....!
BARKA DA SAFIYA
TON Sunyi Partnership da Ethena a Taron Token2049
Ethena wata manhaja ce da aka fara kirkira akan Ethereum, wadda ke samar da synthetic crypto-dollar mai suna USDe.
Wannan USDe ta bambanta da USDT wanda ake (backing) jingina masa darajarsa da ainihin daloli na zahiri, hannayen jari da zinari.
USDe ba shi da irin backing ɗin dana faɗa a sama irin na USDT, sai dai ana daidaita darajarsa ne da na Dala ta hanyar dabarar kasuwa (exchange rate) da amfani da kayan aikin hada-hadar derivatives.
Amfanin USDe kuma ya fi a fili ga masu son cikakken iko da kudinsu tunda a crypto muke: ba za a iya blocking ko freezing na asusunka ko kuɗinka ba kamar yadda ake yi da USDT idan buƙatar hakan ta tashi.
Ethena ta ce an samu daidaiton darajar USDe ne ta hanyar amfani da dabarun delta hedging da kuma damar arbitrage tsakanin saye da fitarwa na USDe.
Al’ummar Ethereum sun rungumi wannan fasaha sosai, kuma ana amfani da shi da yawa a kasuwa.
ENA (token na Ethena) ya shiga cikin Top 48 a CoinMarketCap, yayinda USDe ke cikin Top 26.
Ganin yadda TON suke Partnership da manyan projects a duniya, alamune na sun ɗauki hanyar yin gyara a blockchain ɗinsu sosai.